5 Satumba 2020 - 11:50
Burtaniya Ta Tabbatar Da Bashin Da Kasar Iran Take Binta Na Sayan Makamai

Sakataren harkokin tsaro na kasar Burtaniya ya tabbatar da cewa gwamnatin kasar Iran tana bin kasarsa bashi wanda asalinsa na sayan makamai ne aka soke daga baya.

ABNA24 : Jaridar The Guardian ta nakalto Ben Wallace yana fadar haka a karon farko, ya kuma kara da cewa yawan bashin ya kai Fam miliyon 400 wadanda kasar Iran ta biya don sayan dankunan yaki 1,750 da kuma mutocin soja masu sulke.

Labarin ya kara da cewa bayan nasarar juyin juya halin musulnci a kasar Iran a shekara 1979, da kuma korar Sarki Sha daga kasar gwamnatin Brutaniya ta soke cinikin sannan ba ta biya kasar Iran kudaden ba.

Wata majiya ta kara da cewa a shekara ta 2008 wasu wadanda suka shiga tsakani sun tabbatar da cewa gwamnatin Iran tana bin Burtaniya wadannan kudade kuma bata biyata ba.

Daga baya gwamnatin kasar ta Burtaniya ta yi ta kawo uzurori na kin biyan bashin saboda takunkuman tattalin arziki na zalunci wanda gwamnatin Amurka ta dorawa kasar Iran.

342/